A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da wannan biki ne a ƙarƙashin jagorancin Shareef Alhaji Abdulƙadir Sarkin Baƙi, wanda ke shirya taron Maulidin a kowace shekara. Bikin na bana ya gudana na tsawon kwanaki biyu, daga ranar Asabar zuwa Lahadi, 12 da 13 ga Satumba 2026, a birnin Kano, kamar yadda SK Press TV ta ruwaito.
A wannan shekara, an kawo wani sabon salo wajen gudanar da bikin, inda aka bai wa wasu mutanen da ke ɗauke da sunayen Manzon Allah (S), Imam Ali (AS), Imam Hassan (AS), Imam Husaini (AS), Sayyidi Abdullahi da Sayyid Abudalib, motoci da babura a matsayin kyaututtuka.
Haka kuma, an rarraba kayan ɗinki da sauran kayayyakin amfanin gida ga wasu mutanen da ke ɗauke da sunayen iyalan Manzon Allah (S), ciki har da Sayyida Amina, Sayyida Fatima da Sayyida Khadija (AS).
A wani ɓangare na tallafa wa mabukata, an rarraba sama da buhunan shinkafa 200, domin rage musu wahalhalun rayuwa da kuma sanya farin ciki a zukatansu albarkacin wannan lokaci na Maulidi.
Bugu da ƙari, an karrama wasu mutanen da ke ɗauke da sunayen Khalifofin Manzon Allah (S), inda aka ba su kayayyaki na musamman tare da kyautar kuɗi har Naira 300,000 ga kowane mutum.
Haka kuma, an bai wa Sulaiman S. Uziri kyautar wani babban gida na musamman, a matsayin girmamawa da yabo bisa gudummawar da yake bayarwa wajen yabon Manzon Allah (S) da Ahalinsa.
Taron Maulidin ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban, waɗanda suka haɗa da wa'azi da nasihohi, yabon Manzon Allah (S), karrama mutane da kuma tallafa wa jama'a.
Masu shirya taron sun bayyana bikin a matsayin wata dama ta nuna ƙauna da girmamawa ga Manzon Allah (S) da iyalansa, tare da amfani da wannan lokaci wajen tallafa wa mabukata da faranta ran al'umma.









Ra'ayinka